Gwamnatin Zamfara za ta haɗa hannu da Sweden don bunƙasa jihar
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa a shirye ya ke ya haɗa hannu da ƙasar Sweden a fannoni da dama, waɗanda suka haɗa da ilimi, Harkar lafiya da samar da makamashi. Gwamna Lawal ya furta haka ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin Ambasadar ƙasar Sweden a Nijeriya, Annika Hahn-Englund cikin makon da…
