Ramadan: An Nemi Al’umma Su Tausaya Wa Junansu

Daga Bello Hamza, Abuja

A halin yanzu an bukaci al’umma Musulmi su tabbatar da sun tausayawa al’ummar da suke mu’amala dasu ba tare da nuna bambanci ba, musamman ganin mun shiga wata mai alfarma ta Ramadan watan da ake ninka ladan dukkan ayyukan alhairi da mutum ya yi. Wannan kira ya fito ne daga bakin wani malamin addinin Musulunci kuma shugaban kungiyar masu ilimin taurari na nahiyar Afrika Sheikh Muhajjadina Sani Kano a tattaunawar da ya yi manema labarai a ofishinsa da ke Abuja.

Sheikh Muhajjidina ya bayyana cewa, a wannan watan ana karfafa bukatar ciyarwa a tsakanin al’umma, “wannan kiran ba wai ga masu hannu da shuni kadai ba ne, duk talaucin ka akwai wadanda ka fi su, ya kamata kowa ya duba kasa da shi don ya tallafa”.

Ya ce, tabbas al’umma suna fuskantar matsalolin rayuwa daban-daban, musamman a kan abin da ya shafi abinci da al’amurran yau da kullum, a kan haka ya kamata masu hannu da shuni su samar da kaso na musamman da za su mika wa mabukata da ke kiwaye da su.

“Wannan lokaci ne da ake rigerige wajen ayyukan alhairi tsakanin maza da mata yaro da babba, da masu arziki da talakawa, a kan haka ba wai sai tara dukiya zaka fara ciyarwa ba, a cikin dan abin da Allah ya baka a ciki ne zaka ciyar da mabukata”, in ji shi.

Sheikh Muhajjadina ya yi kira ga al’umma da su hada kai da jami’an tsaro a kokarin da suke yi na kawar da bata gari a cikin al’umma. Ya ce, kamata ya yi a rinka ba jami’an tsaro bayanai masu muhimmanci na al’murran da muka gani zai iya barazana da halin zaman lafiyar da muke ciki. Ya kuma nemi gwamnati a dukkan matakai su yi kokarin sauke nauyin da ke kansu a kan al’ummar da suke mulka. Daga karshe ya yi addu’ar Allah ya karbi dukkan addu’o’imu Ya kuma sa muna cikin ‘yantattun da za su rabauta a cikin wannan watan na Ramadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *