Rundunar Sojan Najeriya ta ce dakarunta na Operation Fansan Yamma na ƙara tsananta bincike domin gano daliban da aka sace a jihohin Neja, Kebbi da Zamfara.
Majiyar tsaro daga Hedikwatar Soja ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa dakarun sun yi nasarar halaka ‘yan ta’adda da kuma lalata sansanoninsu a sassa daban-daban na arewa ta tsakiya da arewa maso yamma cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
A cewar majiyar, dakarun Brigade ta 22 sun fara aikin ne bayan sace ɗaliban makarantar St Mary’s, Papiri, a ƙaramar hukumar Agwara ta jihar Neja, inda aka tura jiragen leƙen asiri (ISR) tare da ƙungiyoyin bincike na ƙasa domin bin sawun maharan.
An faɗaɗa aikin bincike zuwa yankin Audu Fari a ƙaramar hukumar Borgu.
A Mariga kuwa, dakarun FOB Gulbin Boka sun yi wa ‘yan ta’adda kwanton-bauna a kusa da Magaman Daji, lamarin da ya yi sanadiyyar kashe wasu daga cikinsu da kuma kwace babura guda huɗu.
Majiyar ta ce a jihar Kebbi kuma, dakarun da ke ƙoƙarin ceto ɗaliban GGSS Maga da aka sace tun ranar 17 ga Nuwamba sun kaddamar da babban samame a dazukan Gando/Sunke da ke Kebbi da kuma yankin Talata Mafara a Zamfara.
An lalata sansanonin ‘yan ta’adda guda uku, wanda hakan ya tilasta musu guduwa daga maboyarsu. Dakarun sun kuma gano fasfo na wata mata daga Bagega wanda ya ɓace a dajin.
Rundunar sojan ta tabbatar da cewa za ta ci gaba da wannan aiki har sai an kubutar da dukkan ɗaliban da aka sace, tare da tarwatsa hanyoyin sadarwar ‘yan ta’adda a arewa ta tsakiya da arewa maso yamma.
