Sama da mutane 3,300 suka rasu sakamakon girgizar kasa a Myanmar

Yawan mutanen da suka rasu sakamakon girgizar kasa a Myanmar ya wuce 3,300, kamar yadda kafar watsa labarun kasar ta bayyana a ranar Asabar, a yayin da babban mai kula da taimakon jin kai na majalisar dinkin duniya ya sabunta kiransa ga duniya da a taimaki kasar wadda annobar ta afkamawa.

Kamar Press TV ta ruwaito, girgizar kasar ta ranar Litinin ta rusa gine-gine tare da lalata abubuwa a fadin kasar, inda mutane 3,350 suka rasu wasu 4,508 suka jikkata yayin da 220 suka bace kamar yadda sabbin alkaluman kafar watsa labarun cikin gida na kasar ya bayyana.

Sama da mako daya bayan annobar, mutane da dama a kasar ba su da matsugunni, suna barci ne a dole a waje saboda gidajensu sun lalace ko kuma suna tsoron sake rushewarsu, kamar yadda kafar watsa labaru ta France 24 ta ruwaito.

Wata kididdigar majalisar dinkin duniya ta nuna cewa sama da mutane miliyan uku na iya kasancewa wadanda girgizar kasar mai karfin 7.7 ta shafa, wanda hakan ya sa abubuwa suka ta’azzara biyo bayan yakin basasa da ya faru a kasar shekaru hudu da suka gabata.

Babban jami’in taimakon jin kai na majalisar dinkin duniya ya hadu da wadanda al’amarin ya shafa a ranar Asabar a tsakiyar birnin Mandalay da ke kasar Myanmar – wanda yana kusa ne da inda al’amarin ya afku kuma wanda a yanzu ya ke fama da abubuwan da suka lalace a fadin birnin.

“Yanayin rushewar abubuwa da ya afku ba kadan ba ne.” Kamar yadda Tom Fletcher ya wallafa a shafin X.

“Duniya dole ta kawo taimakon ta ga Myanmar.”

Kamar yadda kafar ta France 24 ta ruwaito, kasashen Sin, Rasha da Indiya na daga cikin kasashe na farko da suka kawo taimakon su, inda suka kawo tawagar masu aikin ceto ga Myanmar domin a nemo inda wadanda suka tsira suke.

Amurka ta kasance a gaba wajen bayar da taimako na kasa-da-kasa sakamakon annoba, sai dai shugaban kasa Donald Trump ya dakatar da hukumar samar da agaji ta kasar.

A ranar Juma’a Washington ta bayyana cewa za ta kara dalar Amurka miliyan 7 a kan miliyan 2 da ta bayar tun a farko ga kasar Myanmar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *