Sanarwa ta musamman daga CBN: BDC 82 Kaɗai CBN Ya Bai Wa Lasisin Canjin Kuɗin Ƙasashen Waje

Ashafa Murnai Barkiya

Wata muhimmiyar sanarwar da ta fito daga Babban Bankin Nijeriya (CBN), na ɗauke da cewa kamfanonin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje 82 ne kaɗai bankin ya bai wa lasisin amincewa ya yi hadahadar canjin kuɗaɗen waje, daga ranar 27 ga Nuwamba, 2025.

Cikin wata sanarwar da Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a da Yaɗa Labarai, Hajiya Hakama Ali ta sa wa hannu a ranar Litinin, ta gargaɗi jama’a su guji hulɗa da ‘yan canjin da ba su da lasisi daga CBN.

CBN ya ce an fito da waɗannan sabbin ƙa’idoji ne a ƙarƙashin Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Hadahadar Kuɗi ta 2025, wato ‘Banks and Other Financial Institutions Act’ (BOFIA), 2020, tare Ƙa’idojin Kula da Masu Harkar Canjin Kuɗaɗen Waje na Nijeriya ta 2024, wato ‘Regulatory and Supervisory Guidelines for Bureaux De Change Operations in Nigeria’ 2024.

CBN ya tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, mai ɗauke da sa hannun Hakama Sidi Ali, Daraktar Riƙo a Sashen Sadarwa ta Bankin.

Sanarwar na ɗauke da cewa, kamfanonin canji wato DBC da aka lissafa a shafin yanar gizon CBN kaɗai ne aka amince su fara aiki daga ranar da aka ƙayyade ɗin.

Babban Bankin Nijeriya ya ce zai ci gaba da sabunta jerin BDC ɗin, wato ‘Bureau de Change’ masu sahihin lasisi, domin jama’a su riƙa tantancewa.
Daga nan sai sanarwar ta yi gargaɗin cewa a guji hulɗa da masu musayar kuɗi da ba su da lasisi.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa, “Don kauce wa ruɗani, gudanar da kasuwancin Bureau De Change ba tare da lasisi ba, laifi ne a ƙarƙashin Sashe na 57(1) na BOFIA 2020. Don haka jama’a su kula kuma su bi doka.”

Idan za a iya tunawa, cikin watan Mayun shekarar da ta gabata, CBN ta soke dukkan tsofaffin lasisin nasu canjin kuɗi, tare da umartar cewa su sake neman sabbin lasisi.

An umarce su da su nemi lasisi na ɗaya daga cikin rukuni biyu:

Babban Lasisi: Wannan sai mai babban jari na aƙalla Naira biliyan biliyan biyu, abin da ya yi sama.

Ƙaramin Lasisi: Wannan kuma ana buƙatar babban jari na Naira miliyan500 abin da ya yi sama.

CBN ya ce an ba kowane BDC waadin watanni shida daga ranar sakin ƙa’idojin, domin su cika sharuɗɗan neman lasisi.

A watan Fabrairu 2024, Bankin ya fitar da ƙa’idoji don neman shawarwarin masu ruwa da tsaki.

CBN ya bayyana cewa bayan kammala tattaunawar, ya fitar da ƙa’idojin kula da ayyukan masu canji na 2024, waɗanda duk masu gudanarwa da masu neman kafa BDC a Nijeriya dole ne su tabbatar sun cika kuma suna aiki da su.

CBN ya ce masu babban lasisi za su iya aiki a kowace jiha da da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *