Sanarwar ga yan Najeriya masu sha’awar aiki a fannin tsaro, an bude neman sabbin ’yan sanda 50,000 a Najeriya

Hukumar Kula da Ma’aikatan ’Yan Sanda ta Ƙasa (PSC) tare da Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (NPF) sun sanar da buɗe shafin neman aiki domin ɗaukar sababbin ’yan sanda 50,000, bisa umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Alhamis, 11 ga Disamba 2025, ta ce wannan mataki na daga cikin manufofin gwamnati na ƙarfafa tsaro, inganta aikin ’yan sanda a matakin ƙasa da ƙauyuka, da kuma ƙara yawan jami’an da rundunar ke da su a halin yanzu.

Sharuɗɗan neman aikin

Hukumar ta ce ana buƙatar masu neman aikin su kasance:
• ’Yan Najeriya (Wadanda aka haifa a Najeriya)
• Masu shekaru 18 zuwa 25 (General Duty) ko 18 zuwa 28 (Specialists)
• Masu cikakkiyar lafiya ta jiki da ta tunani
• Tsawon akalla 1.67m ga maza ko 1.64m ga mata (na General Duty)

Ga masu neman General Duty, ana buƙatar akalla Credit biyar a SSCE/NECO ko makamancin sa, ciki har da Turanci da Lissafi.

Masu neman kujerun Specialists kuma na buƙatar Credit huɗu, da ƙwarewa ta aƙalla shekaru uku a fannin da suke nema.

Lokacin buɗe portal

Shafin neman aikin zai kasance a buɗe daga:
Litinin, 15 ga Disamba 2025 zuwa Lahadi, 25 ga Janairu 2026.

Dukkan waɗanda ke sha’awar neman aikin za su yi hakan ta yanar gizo kawai a shafin:
www.npfapplication.psc.gov.ng

Hukumar ta ja hankalin jama’a da cewa tsarin bai ƙunshi biyan ko sisin kuɗi ba, tana gargadin mutane su yi hattara da masu damfara da ke fakewa da aikin ɗaukar ma’aikata.

Kira ga ’yan ƙasa

PSC ta yi kira ga dukkan matasa da suka cancanta da kishin ƙasa da su yi amfani da wannan dama domin bayar da gudummawa wajen inganta tsaron Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *