Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce yawaitar sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC na bayyana raunin da ke cikin jam’iyyun adawa, yayin da APC ke ƙara ƙarfi.
Shettima ya bayyana haka ne a Enugu, inda ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron maraba da Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu, tare da wasu ‘yan majalisar sa da magoya bayansa, da suka koma APC daga PDP.
A cewarsa, “hanyoyin da APC ta shimfiɗa sun zama gadar haɗin kai, yayin da jam’iyyun adawa ke fuskantar ɓarakar da suka gina da hannayensu.”
Ya kara da cewa tsarin shugabancin Tinubu, wanda ke da sauraro kowa da ɗaukar kowa babu wariya, shi ya mayar da APC jam’iyya mafi ƙarfi a nahiyar Afirka.
Shettima ya kuma bayyana Gwamna Mbah a matsayin wanda “tun da dadewa yake mai kishin cigaba,” yana mai cewa da alama ya dade da buya da tsintsiya a cikin alamar jam’iyyarsa ta umbrella (PDP).
“Yanzu da ka fito fili, za ka jagoranci gina APC a Jihar Enugu, kuma kana da goyon bayan shugaban ƙasa da jam’iyya baki ɗaya,” in ji shi.
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya ce zuwan Gwamna Mbah da magoya bayansa ya nuna cewa APC ce “gida na gaske ga masu kishin ci gaba.”
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, duka sun yaba da sauya shekar Gwamna Mbah, suna masu cewa hakan ya nuna sabon shafi ga siyasar yankin Kudu maso Gabas.
A nasa jawabin, Gwamna Mbah ya ce matakin da suka ɗauka na shiga APC ba na shi kaɗai ba ne, illa alƙiblar da dukan jam’iyyarsa da magoya bayansa suka amince da ita.
Ya ce: “Yau mun yanke shawara tare da haɗin kai, domin mu samu damar shiga sahun gaba a siyasar ƙasa. APC ce babbar jam’iyya a Afirka, kuma yanzu mun dawo gida.”
Gwamna Hope Uzodinma na Imo, wanda ke jagorantar kungiyar gwamnonin APC, ya ce shigar Enugu cikin APC zai ƙara ƙarfafa matsayin shugaban ƙasa a yankin Kudu maso Gabas da siyasar ƙasa baki ɗaya.