Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya kan Tattalin Arziki, Muhammad Sani Abdullahi, ya bayyana cewa Sauye-Sauyen da aka gudanar a cikin Babban Bankin Najeriya (CBN), ba ayi su dan tsangwamar wasu ba ko cire mutane bisa son rai, tsari ne na daidaita ma’aikata da sake fasalin aiki bisa bukatar da ake da ita a babban bankin.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyin da aka yi a taron da Sir Ahmadu Bello Memorial foundation suka shirya na tattaunawa tsakanin gwanati da al’umma a Jihar Kaduna a ranar alhamis data gabata.
Ya bayyana cewa daga shekarar 2019 zuwa 2023, an dauki ma’aikata 4,000, wanda ya kai yawan ma’aikatan babban bankin daga 5,000 zuwa fiye da 9,000. Ya bayyana cewa hakan ya janyo cunkoso a ofisoshin Abuja har ta kai ana amfani da dakunan taro a matsayin ofis. Ya kara da cewa hakan ya jawo hatta kamfanonin inshora suka ki bayar da inshora saboda toshe hanyoyin fita na gaggawa.
“Mun duba me ake bukata a Abuja? Me muke bukata a Legas? Da sauran jihohi. Sai muka raba ma’aikatan mu yadda zai dace da bukatun kowanne reshe na ofishin mu.”
Dangane da korafin wasu da aka mayar da su Legas ko Kaduna, ya ce ba wata manufa ce ta nuna wariya a hakan, domin daga ciki har da ɗan Sakataren Gwamnatin Tarayya wanda a yanzu haka an mayar da shi Legas.
Har wa yau, ya bayyana cewa shirin (Early Exit) ficewa daga aiki da wuri shiri ne da ma’aikatan da ke kasa ne suka nemi a kafa shi, domin su iya samun sabbin damammaki. Ya kawo misali da wasu ma’aikata guda hudu da suka taru don kafa bankin microfinance daga kudin da suka samu daga ficewar.
“Wannan dama ce ga wadanda ke son su nemi wata hanyar rayuwa daban. Ba wani dan siyasa ko yanki aka nufa da shi ba.”
A kan zargin da wasu suka yi cewa an nada daraktoci 16 daga wani yanki daya, ya ce wannan ba gaskiya ba ne:
“An bi tsari na gaskiya wanda kamfanin PricewaterhouseCoopers ya jagoranta, kuma akwai daraktoci da dama daga Arewa da aka nada, masu inganci, kuma za a bayyana su nan gaba.”
Ya kuma yi kira ga jama’a da su bada goyon bayan su domin ci gaba da kawo sauye-sauye a babban bankin bisa gaskiya da adalci.