Sauye-sauyen da na kawo sun fara haifar da ɗa mai ido – Tinubu a jawabin cika shekaru biyu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa ta cimma muhimman nasarori a cikin shekaru biyu da suka gabata tun bayan hawan sa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023. A cikin jawabin sa ga jama’ar ƙasa a yau domin cikar shekara biyu da mulki, Shugaba Tinubu ya jaddada cewa sauye-sauyen da ya kawo sun fara haifar da ɗa mai ido ga ’yan Nijeriya.

Babban Sauyi a Tattalin Arziki

Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da Shugaban Ƙasa ya bayyana shi ne cire tallafin fetur da kawar da tsarin musayar kuɗin waje da ake a matakai da dama. Ya ce waɗannan matakai sun hana ƙasar faɗawa cikin matsanancin halin karyewar darajar kuɗi da matsin tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa, “Tattalin arzikin mu yana dawowa hayyacin sa. Farashin abinci irin su shinkafa yana ƙara sauka, kuma masana’antar man fetur din mu ta farfaɗo da sabbin jarin da suka kai dala biliyan takwas a shekarar 2025.”

Riba a Fannin Kuɗi da Haraji

Shugaban ya bayyana cewa gwamnatin sa ta rage gibin kasafin kuɗi daga kashi 5.4% a 2023 zuwa 3% a 2024. Haka kuma, bashin an biya bashin IMF gaba ɗaya, kuma asusun ajiyar kuɗin waje ya ƙaru daga dala biliyan 4 a 2023 zuwa dala biliyan 23 a ƙarshen 2024.

A fannin haraji, Tinubu ya ce an samu ƙarin kuɗin shiga inda haraji da GDP suka ƙaru daga 10% zuwa 13.5% a shekara guda. Ya ce an ware kayan abinci, kiwon lafiya da ilimi daga abubuwan da za ake biya musu haraji (VAT), domin rage radadin da tsadar rayuwa ga talakawa.

Lafiya da Ilimi

A ɓangaren lafiya, Shugaba Tinubu ya ce an sabunta cibiyoyin lafiya fiye da 1,000, sannan ana ci gaba da gyara wasu 5,500. Akwai cibiyoyin jinyar cutar daji guda shida da aka kafa, sannan an ƙara yawan waɗanda suka shiga tsarin inshorar lafiya daga miliyan 16 zuwa miliyan 20.

A fannin ilimi, gwamnatin ta ƙaddamar da tsarin bashi ga dalibai domin ba da dama ga marasa galihu su samu karatu a jami’o’i da kwalejojin gaba da sakandare.

Tsaro da Ayyukan Soji

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatin sa ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, wanda hakan ya taimaka wajen rage hare-hare a wasu sassan Arewa-maso-yamma da dawo da noma da zirga-zirga a hanyoyin da suka daɗe suna fama da barazanar ’yan bindiga.

Matasa da Sana’a

A ɓangaren matasa, ya ce an ɓullo da shirye-shirye na koyar da sana’o’i da ba da tallafi ga ƙananan ‘yan kasuwa da masu ƙirƙire-ƙirƙire. Ya bayyana cewa cibiyar NASENI tana jagorantar ƙirƙire-ƙirƙire da horar da matasa kan sana’o’i irin su ƙera motocin lantarki da amfani da jirgi mara matuƙi (drone).

Noma Da Abinci

A ɓangaren noma, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa an sayo dubban injinan noman zamani da taki domin ƙara yawan amfanin gona da rage tsadar abinci.

Gina Hanyoyi Da Wutar Lantarki

Gwamnatin ta ci gaba da gina manyan hanyoyi kamar su hanyar Abuja-Kano, hanyar Bakin Teku ta Legas-Kalaba da sauran su. Haka kuma, ana inganta wutar lantarki ta hanyar amfani da hasken rana da gyaran tashoshin wutar lantarki.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa duk da ƙalubalen da ake fuskanta, akwai kyakkyawar makoma ga Nijeriya.

“Muna kan hanya madaidaiciya. Da yardar Allah, mun yi bankwana da mummunan yanayin da muke ciki na baya. Alƙawarin mu na gina Nijeriya mai ƙarfi da haɗin kai yana ci gaba da karɓuwa,” in ji shi.

Shugaba Tinubu ya kammala da godiya ga ɗaukacin ‘yan Nijeriya bisa juriya da goyon baya, yana mai roƙon Allah ya ci gaba da albarkatar ‘yan Nijeriya da Nijeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *