Sauye-sauyen tattalin arzikin Tinubu suna daidaita Nijeriya — Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake aiwatarwa suna daidaita tattalin arzikin Nijeriya, maido da amincewar jama’a, tare da sanya ƙasar nan kan tafarkin cigaba mai ɗorewa bayan shekaru da dama na rashin tabbas.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata hira ta kafar intanet a shirin ICAN On Air, wanda Ƙungiyar Ƙwararrun Akantoci ta Nijeriya (ICAN) ta gabatar, a ranar Alhamis.

A cewar sa, cire tallafin man fetur da kuma haɗe farashin musayar kuɗaɗen ƙasashen waje matakai ne da aka ɗauka tun da wuri domin magance raunin da tattalin arzikin ƙasar nan yake da shi tun fil’azal.

Ya ce: “Ba za ka iya gina tattalin arziki a kan harsashi mai matuƙar rauni ba. Ya zuwa watan Mayu 2023, kusan jihohi 26 cikin 36 ba su iya biyan albashi, sannan kusan kashi 97 na kuɗaɗen shigar Nijeriya suna tafiya ne wajen biyan bashi. Nijeriya ba za ta iya ɗorewa a kan wannan turbar ba.”

A cewar Ministan, ko da yake waɗannan sauye-sauyen sun haifar da matsaloli na ɗan lokaci, sun zama dole ne domin gyara kurakurai na tsawon lokaci da kuma tabbatar da cewa arzikin ƙasa ya amfani ɗaukacin jama’a maimakon wasu tsirarun mutane.

A cewar sa: “Waɗannan ba matakai ne masu sauƙin ɗauka ba ta fuskar siyasa, amma Shugaban Ƙasa ya yi imanin cewa muna rayuwa ne cikin yanayi na jira-ta-fashe. Idan ba a ɗauki waɗannan matakan ba, lallai Nijeriya na tafiya ne a kan turba mara kyau.”

Idris ya ce alamomin tattalin arziki na baya-bayan nan sun nuna cigaba na gaske, ciki har da ƙaruwa a ajiyar kuɗaɗen waje, raguwa a hauhawar farashi, da ƙaruwar ƙwarin gwiwar masu zuba jari

Ya ce: “A yau, ajiyar kuɗaɗen waje ta Nijeriya ta kai kusan dala biliyan 46, mafi girma cikin kusan shekaru takwas. Hauhawar farashi ta ragu matuƙa, kuma Nijeriya tana samun karɓuwa a gida da kuma a ƙasashen waje.”

Game da batun gyaran haraji, Ministan ya fayyace cewa manufar ba wai ɗora wa ’yan ƙasa ƙarin nauyi ba ne, nufin gwamnati shi ne sauƙaƙa tsarin, kawar da maimaita biyan haraji, da shigar da mutane da dama cikin tsarin biyan harajin.

Ya ce: “Sauye-sauyen haraji ba wai domin mutane su riƙa biyan haraji mai yawa ba ne. Manufar sa ita ce sauƙaƙe tsarin, kawar da maimaituwa, da kuma shigo da waɗanda ba sa biya cikin tsarin, domin gwamnati ta sami damar tsara ayyukan cigaba yadda ya kamata.”

Ministan ya jaddada cewa amana ita ce ginshiƙin shugabanci nagari da sadarwar gwamnati, yana mai cewa ita ce babban abin da ya sa a gaba tun lokacin da ya kama aiki.

Ya ce: “Ba tare da amana ba, ba za a iya gina ƙwarin gwiwa ba, kuma idan babu ƙwarin gwiwa, babu cigaba na gaske. Aikin mu shi ne mu bayyana manufofin gwamnati cikin gaskiya, tare da sauraron ra’ayoyin ’yan Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa Tinubu yana neman jin ra’ayoyin jama’a a kai a kai game da manufofin gwamnati, kuma a shirye yake ya gyara yadda ake aiwatar da su idan buƙatar hakan ta taso, amma yana tsayawa daram kan sauye-sauyen da yake ganin suna da muhimmanci ga cigaban ƙasa na dogon lokaci.

Game da yaɗuwar labaran ƙarya, Ministan ya ce gwamnati tana ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da wayar da kan jama’a kan ilimin kafofin watsa labarai domin rage tasirin labaran ƙarya ba tare da tauye ’yancin faɗar albarkacin baki ba.

Ya ce: “Labaran ƙarya suna da matuƙar haɗari. Idan ba ka samo hanyar rage tasirin su ba, wata rana za ka wayi gari ba ka da ƙasa. ’Yancin kafofin watsa labarai na da muhimmanci, amma dole ne a yi amfani da ‘yancin yadda ya dace.”

Idris ya kuma bayyana cewa Nijeriya ta samu nasarar karɓar baƙuncin Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai ta UNESCO, wadda za ta taimaka wajen bai wa ’yan ƙasa, musamman matasa, ƙwarewar bambance gaskiya da ƙarya.

Ministan ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ci gaba da haƙuri da haɗin kai yayin da ake aiwatar da sauye-sauyen, yana mai tabbatar da cewa amfanin su zai ƙara bayyana a fannonin ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya, da cigaban jihohi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *