SHIRIN ƘARFAFA JARIN BANKUNA: CBN ya shawarci bankunan da ba su da ƙarfi su haɗe ko su rage wa lasisin su geji

Ashafa Murnai Barkiya

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya yi magana dangane da ƙoƙarin da bankuna ke yi domin ganin sun cika sharuɗɗan adadin ƙarfin jari da CBN ya gindaya masu.

Ya ce da yin hakan zai sa a guje wa sake maimata kura-kuran da aka taɓa yi can a baya.

“Mun bai wa bankunan kasuwanci isasshen lokaci da kuma zaɓi domin ganin sun cika sharuɗɗan da aka gindaya masu. Saboda haka ba wani abin tayar da hankali ko razana a nan.” Inji Cardoso.

Da yake magana kan batun tsare-tsaren inganta tattalin arziki, kuɗaɗen ruwa da kuma taƙaita karɓar lamuni daga masu kasuwanci, gwamnan ya ce tilas batun bunƙasa tattalin arziki mai ɗorewa shi ne farkon abin dubawa, kafin a yi maganar batun ramce mai karsashi.

“Domin idan tattalin arziki bai samu nagartaccen tushe ko tubali na, to samun ci gaba ba zai yiwu ba. Maganar cewa kuɗin ruwa ya yi tsada kuma haka ɗin ne, amma tunda tattalin arziki ya hau kan miƙaƙƙar hanya, za a sassauta kuɗin ruwan.”

Ya yi wannan jawabi wurin taron da London Business School tare da haɗin guiwar JP Morgan da Goldman Sachs suka shirya.

A wani labarin kuma, Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Wale Edun, ya jinjina wa Gwamnan CBN, Cardoso, dangane da nasarorin da yake samu wajen aiwatar da tsare-tsaren tattalin arzikin ƙasa masu tasirin daƙile tsadar rayuwa da kuma taka wa hauhawar farashin kayayyaki burki.

Edun ya yi bayanin a wurin taron da Cibiyar Chartered Institute of Bankers of Nigeria (CIBN) ta shirya, a Legas.

Ya ce CBN na ƙoƙari matuƙa wajen dawo wa tattalin arzikin Nijeriya da tsarin hada-hadar kuɗaɗe darajar su a idon masu zuba jari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *