- Sanata Barau ya yabawa Shugaba Tinubu bisa amincewa Kudurin sa na mayar da Federal Polytechnic Kano zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Tarayya, Kabo.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana godiyarsa ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bisa amincewarsa da kudirin da ya gabatar a Majalisa na sauya Federal Polytechnic Kabo zuwa Federal University of Science and Technology, Kabo a Jihar Kano.
Amincewar ta zo ne cikin wata wasika da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya aikewa Majalisar Dattawa a safiyar yau, wadda shugaban Majalisar Godswill Obot Akpabio ya karanta a zauren Majalisar.
“Wannan mataki ya nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen bunkasa damar samun ilimi mai zurfi da kuma gaggauta samar da ci gaban ƙasa ta hanyar samar da ƙwarewar da matasanmu ke bukata,” in ji Sanata Barau.
Ya bayyana cewa sauya kwalejin zuwa jami’ar kimiyya da fasaha ya yi daidai da yadda duniya ke tafiya wajen bunkasa cigaban dan Adam, da kuma bai wa matasa damar shiga sahun ci gaba a fannin kimiyya da fasaha kamar Artificial Intelligence, Robotics, da Cybersecurity.
“Matasan Najeriya su ne ginshikan ci gaban al’umma, kuma ilimin zamani yana da matukar muhimmanci wajen samar da ci gaba a kowace kasa. Wannan jami’a za ta zama cibiyar koyar da sabbin fasahohi da kimiyya,” in ji shi.
Hakazalika, Sanata Barau ya taya shugabanni, ma’aikata, dalibai da al’ummar da ke kewaye da Federal Polytechnic Kabo murna da wannan ci gaba mai tarihi. Ya kuma bukace su da su ci gaba da rike kima da darajar ilimi yayin da suke shirin shiga sabon mataki na zama jami’a.
Ya kara da cewa wannan mataki wani babban ci gaba ne ga yankin da kuma kasa baki daya, yana mai yabawa shugabancin Shugaba Tinubu bisa hangen nesa da jajircewarsa wajen ganin Najeriya ta ci gaba.
“Muna godiya, mai girma Shugaban Ƙasa, bisa irin wannan jagoranci na hangen nesa da jajircewa wajen gina ƙasa. Allah ya saka da alheri,” in ji Sanata Barau.