Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro tare da ba da umarni ga jami’an tsaro da su ɗauki ƙarin ma’aikata

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a fadin kasar, tare da bayar da umarnin daukar karin jami’an tsaro da zummar karfafa yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban kasa da aka fitar ranar Laraba, Shugaba Tinubu ya ce wannan mataki ya zama dole ne sakamakon yadda sabbin hare-hare ke ci gaba da faruwa a wasu jihohin arewacin kasar.

Shugaban ya ce rundunar ‘yan sanda za ta dauki karin ’yan sanda 20,000, lamarin da zai kara yawan wadanda za su shiga aiki zuwa 50,000 gaba daya. Ya kara da cewa an ba hukumar ‘yan sanda izinin amfani da sansanonin masu bautar ƙasa (NYSC) a matsayin cibiyoyin horaswa na wucin gadi.

Shugaban ya kuma bayar da umarnin cewa jami’an da aka cire daga aikin tsaron fitattun mutane su sake samun horaswa ta musamman kafin a tura su yankunan da ke fama da matsalar tsaro.

A bangaren hukumar DSS kuwa, shugaban kasar ya ba da izinin tura duka rundunonin forest guards da aka horar domin fatattakar ’yan ta’adda da ’yan bindiga da ke boye a dazukan kasar, tare da umarnin daukar karin ma’aikata domin kara mamaye wuraren da ake zargin masu aikata laifuka na fakewa.

Shugaba Tinubu ya ce wannan mataki yana nuni da cewa gwamnati ba za ta lamunci duk wani yanayi da zai bata tsaron kasa ba, tare da jadadda cewa “ba za a sake samun wani wurin boyewa ga miyagu ba.”

Shugaban ya jinjinawa jami’an tsaro kan ceto dalibai 24 da aka sace a jihar Kebbi da kuma mambobin coci 38 da aka kubutar a jihar Kwara, tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da kokarin ceto sauran wadanda ake tsare da su a jihar Neja da wasu sassa na kasar.

Ya kuma bukaci hafsoshin soji su ci gaba da nuna jajircewa da bin ka’idojin aiki, yana mai cewa babu wani sassauci da za a yi wajen hukunta masana aikata laifi ko wadanda ba su cika ka’ida ba.

A cikin jawabin nasa, shugaban ya bukaci Majalisar Dokoki ta kasa da ta fara nazarin dokokin da za su bai wa jihohin da suke bukata damar kafa rundunar ’yan sanda ta jiha.

Ya kuma gargadi jihohi da su yi taka-tsantsan wajen bude makarantu a yankunan da ba su da isasshen tsaro, tare da shawartar masallatai da majami’u a yankunan da ke da matsalar tsaro da su nemi kariyar jami’an tsaro kafin gudanar da ibada.

Tinubu ya jaddada cewa gwamnati ta kafa Ma’aikatar kiwon dabbobi ne domin magance rikicin manoma da makiyaya, yana mai kiran kungiyoyin makiyaya da su rungumi tsarin kiwo a ruga maimakon yawo da dabbobi a fili, tare da mika duk wasu makamai da ba su da lasisi.

Shugaban ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren da suka faru kwanan nan a jihohin Kebbi, Borno, Zamfara, Neja, Yobe da Kwara, tare da tunawa da jami’an soji da suka rasa rayukansu, ciki har da Janar Musa Uba.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su kwantar da hankali, su kasance cikin shiri, tare da ba da hadin kai wajen bayar da bayanai ga jami’an tsaro.

“Wannan lokaci ne da ya bukaci mu hadu guri daya domin kare kasa. Kada mu fada cikin fargaba. Tare za mu iya, tare za mu ci nasara,” in ji shugaban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *