Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa na janye dukkan jami’an ‘yan sandan da ke aiki a matsayin masu gadi ga Manyan Mutane (VVIP/VIP) a fadin kasar nan, domin mayar da su kan ainihin ayyukan tsaro da suka shafe su.
Wannan umarni ya fito ne bayan taron tsaro da shugaban kasar ya jagoranta a ranar Lahadi a Abuja, inda ya tattauna da manyan hafsoshin tsaro, ciki har da rundunar sojin kasa, sojin saman Najeriya, hukumar DSS da kuma Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.
A cewar umarnin shugaban kasar, daga yanzu duk wani VIP da yake bukatar tsaro zai nemi jami’ai daga Hukumar Tsaro ta Civil Defence (NSCDC), wadanda za su rika ba su kariya cikin shiri da makamai.
A halin yanzu, yankuna da dama, musamman kauyuka da wuraren da ke da nisa daga birane, suna fama da karancin jami’an ‘yan sanda a ofisoshin su, lamarin da ya hana su yin aiki yadda ya kamata wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa yana da burin ganin an kara yawan jami’an ‘yan sanda a ko’ina cikin kasar domin magance matsalolin tsaro da suka addabi kasar nan.
Tun da farko, gwamnatin tarayya ta amince da daukar karin jami’an ‘yan sanda 30,000, tare da hadin gwiwar jihohi domin inganta cibiyoyin horas da ‘yan sanda a fadin Najeriya.
