Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ranar Talata ya bai wa Bill Gates, Co-Chairman na Gidauniyar Bill da Melinda Gates, lambar girmamawa ta Commander of the Federal Republic (CFR), a matsayin yabo da godiya ga gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya musamman a fannin lafiya, ilimi, noma da kare lafiyar yara.
A lokacin da yake karɓar bakuncin Bill Gates a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, Shugaba Tinubu ya jinjina wa ayyukan gidauniyar da suka taimaka wajen kawar da cutar shan inna (polio), yaki da zazzabin cizon sauro, da karfafa matasa da mata. Taron ya kuma zama dama ta tattaunawa kan karin hadin gwiwa musamman a fannin amfani da fasaha don inganta lafiya da kirkire-kirkire.
Wannan girmamawa ta nuna yadda gwamnatin Tinubu ke da niyyar ci gaba da hadin gwiwa da abokan hulɗar duniya wajen kawo sauyi ga rayuwar ‘yan Najeriya, musamman talakawa da marasa galihu.