SHUGABA TINUBU YA KARRAMA MANYAN ’YAN RAJIN DEMOKRAƊIYYA DA LAMBAR YABO A RANAR DIMOKURADIYYA

A wani bangare na bikin Ranar Dimokuradiyya da aka gudanar a zauren Majalisar Tarayya dake Abuja, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da lambobin yabo ga wasu fitattun ’yan Najeriya da suka bada gagarumar gudummawa wajen ci gaban dimokuradiyya, zaman lafiya da cigaban ƙasa baki ɗaya.

Shugaba Tinubu ya ce an ware wannan lokacin ne domin karrama waɗanda suka nuna kishin ƙasa ta hanyar hidimar al’umma da gaskiya a cikin shugabanci, aikin tuƙuru, da kare martabar Najeriya a gida da waje.

“Lambobin yabo da muke bayarwa yau ba wai yabo bane kawai, alamar godiya ce da girmamawa ga waɗanda suka zubar da jininsu, sukai amfani da hikimarsu, da bada lokacinsu wajen tabbatar da cewa dimokuradiyyar Najeriya ta kafu bisa doka da gaskiya,” in ji Shugaban Ƙasa.

Daga cikin waɗanda aka karrama akwai Kudirat Abiola (CFR), Shehu Musa Yar’Adua (GCFR), Prof. Humphrey Nwosu (CON), Rear Admiral Ndubuisi Kanu (CON), Alhaji Balarabe Musa (CFR), Pa. Alfred Rewani (CFR), Bagauda Kaltho (OON), Chima Ubani (OON), Dr. Beko Ransome-Kuti (CON), Alao Aka Bashorun (CON), Chief Frank Kokori (CON), Emma Ezeazu (OON), Bamidele Aturu (OON), Fredrick Fasehun (CON), Professor Festus Iyayi (CON), Dr John Yima Sen (OON), Alhaja Sawaba Gambo (CON), Dr. Edwin Madunagu (CON), Dr. Alex Ibru (CON), Chief Bola Ige (CFR), Pa. Reuben Fasoranti (CFR), Sen. Ayo Fasanmi (CON), Sen. Polycarp Nwite (CON) and Dr. Nurudeen Olowopopo (CON).

Hakazalika, ya ƙara da Prof. Wole Soyinka (GCON), Prof. Olatunji Dare (CON), Kunle Ajibade (OON); Nosa Igiebor (OON), Dapo Olorunyomi (OON), Bayo Onanuga (CON), Ayo Obe (OON), Dare Babarinsa (CON), Bishop Matthew Hassan Kukah (CON), Senator Shehu Sani (CON), Gwamna Uba Sani (CON), Barrister Femi Falana, SAN (CON), Prof. Shafideen Amuwo (CON), Barrister Luke Aghanenu (OON), Senator Tokunbo Afikuyomi (CON), Hon. Labaran Maku (OON), Dr. Tunji Alausa (CON), Mr Nick Dazang (OON), Hon Abdul Oroh (OON), Odia Ofeimun (CON), Seye Kehinde (OON), Barrister Felix Morka (CON) Barrister Ledum Mitee (CON), Hon. Olawale Osun (CON), Dr. Amos Akingba (CON), Prof. Segun Gbadegesin (CON), Mobolaji Akinyemi (CFR), Dr. Kayode Shonoiki (CON), Prof. Julius Ihonvbere (CON), Prof. Bayo Williams (CON), Sen. Abu Ibrahim (CFR), da kuma Sen. Ame Ebute (CFR).

Ya kuma ƙara da Uncle Sam Amuka Pemu (CON), Ken Saro Wiwa (CON), Saturday Dobee (OON), Nordu Eawo (OON), Daniel Gbooko (OON), Paul Levera (OON), Felix Nuate (OON), Baribor Bera (OON), Barinem Kiobel (OON), and John Kpuine (OON).

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *