Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sunayen karin mutane 32 da ya zaɓa domin zama jakadu zuwa majalisar dattawa, mako guda bayan tura sunayen farko na mutum uku.
A cikin wasu wasiku guda biyu da aka karanta a zaman majalisar, Shugaba Tinubu ya roƙi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da majalisa ta hanzarta tantancewa tare da tabbatar da mutane 15 a matsayin jakadu (Career Ambassadors), sannan 17 a matsayin jakadu marasa aikin diflomasiyya kai tsaye (non-career).
A cikin jerin sunayen Jakadun (Career Ambassadors) akwai mata huɗu, yayin da mata shida ke cikin rukuni na (Non career).
Daga cikin waɗanda aka zaɓa a matsayin jakadu (non-career) akwai tsohon mai bai wa shugaban ƙasa shawara, Barrister Ogbonnaya Kalu daga Abia; Reno Omokri daga Delta; tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC, Farfesa Mahmud Yakubu; tsohuwar uwargidar jihar Ekiti, Erelu Angela Adebayo; da tsohon gwamnan Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi.
Sauran sunayen sun haɗa da tsohon kakakin majalisar dokokin Katsina, Tasiu Musa Maigari; Yakubu N. Gambo daga Jihar Filato; da tsohon mataimakin babban sakataren hukumar UBEC.
Haka kuma akwai Farfesa Nora Ladi Daduut daga Filato; tsohon mataimakin gwamnan Legas, Otunba Femi Pedro; tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode; da Barrister Nkechi Linda Ufochukwu daga Anambra.
Sauran sun haɗa da tsohuwar uwargidar Oyo, Fatima Florence Ajimobi; tsohuwar kwamishinar Legas, Lola Akande; tsohuwar Sanata daga Adamawa, Grace Bent; tsohon gwamnan Abia, Victor Okezie Ikpeazu; Sanata Jimoh Ibrahim daga Ondo; da tsohon jakadan Najeriya a Vatican, Paul Oga Adikwu daga Benue.
A jerin (career Ambassadors) kuma akwai Enebechi Monica Okwuchukwu (Abia), Yakubu Nyaku Danladi (Taraba), Maimuna Ibrahim Besto (Adamawa), Musa Musa Abubakar (Kebbi), Syndoph Paebi Endoni (Bayelsa), Chima Geoffrey Lioma David (Ebonyi), da Mopelola Adeola-Ibrahim (Ogun).
Sauran sunayen sun haɗa da Abimbola Samuel Reuben (Ondo), Yvonne Ehinosen Odumah (Edo), Hamza Mohammed Salau (Niger), Shehu Barde (Katsina), Ahmed Mohammed Monguno (Borno), Muhammad Saidu Dahiru (Kaduna), Olatunji Ahmed Sulu Gambari (Kwara) da Wahab Adekola Akande (Osun).
Ana sa ran za a tura sabbin jakadan zuwa ƙasashen da Najeriya ke da muhimman hulɗa da su, ciki har da China, India, South Korea, Canada, Mexico, UAE, Qatar, South Africa, Kenya, da kuma manyan ofisoshin wakilai na dindindin kamar na Majalisar Dinkin Duniya, UNESCO da Kungiyar Tarayyar Afirka. Za a bayyana wuraren aikinsu bayan majalisar ta kammala tantance su.
A makon da ya gabata ne Shugaba Tinubu ya tura sunayen mutane uku na farko, wato Ambassador Ayodele Oke (Oyo), Ambassador Amin Mohammed Dalhatu (Jigawa), da Retired Colonel Lateef Kayode Are (Ogun), waɗanda ake sa ran za a tura su zuwa Birtaniya, Amurka ko Faransa bayan tantancewa.
Shugaban ƙasa ya ce nan gaba za a sanar da karin sunaye na jerin sabbin jakadu.
