Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya mika sunan tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, ga majalisar dattawa domin tabbatar da shi a matsayin sabon Ministan Tsaro, bayan murabus din Alhaji Mohammed Badaru Abubakar.
A wata wasika da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya ce nadin Janar Musa ya biyo bayan ajiye aikinsa da Badaru ya yi a ranar Litinin saboda matsalolin lafiya.
Janar Musa, mai shekaru 58 da haihuwa a ranar 25 ga Disamba, ya kasance ɗaya daga cikin manyan hafsoshin soja da suka yi fice a ayyukan soja tun bayan shiga rundunar a shekarar 1991. Ya kasance Babban Hafsan Tsaro daga 2023 zuwa watan Oktoban 2025, tare da samun kyaututtuka da dama ciki har da Colin Powell Award for Soldiering a 2012.
An haife shi a Sokoto a 1967, inda ya yi karatunsa na firamare da sakandire, kafin ya tafi Kwalejin Nazari ta Zariya. Daga nan ya shiga Makarantar Horar da Sojoji ta NDA a 1986, inda ya kammala digirinsa a 1991.
Tun daga lokacin, Janar Musa ya rike mukamai da dama a rundunar soja, ciki har da Babban Jami’i mai lura da horo da ayyuka a Hedikwatar Runduna ta 81, Kwamandan Bataliya ta 73, da Mataimakin Darakta a Sashen Tsare-tsaren Runduna.
A 2019 ya jagoranci Sector 3 na Operation Lafiya Dole da kuma Multinational Joint Task Force a yankin Tafkin Chadi. Daga bisani, a 2021, aka nada shi Kwamandan Operation Hadin Kai, sannan ya jagoranci Rundunar Infantry kafin Shugaba Tinubu ya nada shi Babban Hafsan Tsaro a 2023.
A wasikar da ya aika majalisa, Shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Janar Musa zai kara karfafawa Ma’aikatar Tsaro gwiwa tare da taimaka wa gwamnati wajen inganta tsaron kasa.
