Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Ambasada Ismail Abba Yusuf a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Darakta (Chairman/CEO) na Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON).
Naɗin na jiran amincewar Majalisar Dattawa kamar yadda Sashe na 3(2) na Dokar NAHCON ta shekarar 2026 ya tanada.
A cikin wasiƙar da ya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, a yau, Shugaba Tinubu ya buƙaci a gaggauta tabbatar da naɗin Ambasada Yusuf domin maye gurbin Farfesa Abdullahi Usman, wanda ya yi murabus a wannan makon bayan kusan watanni 14 yana jagorantar hukumar.
Ambasada Ismail Abba Yusuf gogaggen jami’in diflomasiyya ne na Najeriya. Ya taɓa zama Jakadan Najeriya na Musamman kuma Cikakken Wakili a Jamhuriyar Türkiye daga shekarar 2021 zuwa 2024.
Ana sa ran sabon shugaban zai kawo ƙwarewarsa da gogewarsa a harkokin hulɗar ƙasashen waje domin inganta ayyukan NAHCON, musamman wajen shirya aikin Hajji cikin tsari da nagarta.
