SHUGABA TINUBU YA NADA ENGR. RAMAT A MATSAYIN SABON SHUGABA KUMA BABBAN JAMI’IN GUDANARWA NA NERC

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana nada Engr. Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Hukumar Kula da Harkokin Wutar Lantarki ta Ƙasa (NERC). Engr. Ramat, mai shekaru 39 da haihuwa, kwararren injiniya ne a fannin lantarki, kuma yana da digiri na uku (PhD) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare.

Haka zalika, Shugaba Tinubu ya kuma mika sunayen wasu mutane biyu domin a tantance su a matsayin kwamishinonin hukumar NERC. Wadanda aka nada su ne, Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Masu Amfani da Wutar Lantarki, da Dr Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa. Dukkan nade-naden suna jiran amincewar Majalisar Dattawa kamar yadda doka ta tanada.

Sai dai domin kaucewa gibi a shugabancin hukumar, Shugaban Ƙasa ya umarci Engr. Ramat da ya fara aiki a matsayin mukaddashin Shugaba har sai lokacin da Majalisar Dattawa za ta tabbatar da nadinsa. Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin da su yi amfani da ilimi da kwarewarsu wajen ciyar da bangaren wutar lantarki gaba tare da aiwatar da manufofin gwamnati a wannan fanni mai muhimmanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *