Shugaba Bola Tinubu ya sabunta nadin Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa Mai Ritaya, a matsayin Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) na tsawon wa’adin shekaru biyar, a cewar wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa a Abuja ranar Juma’a.
Marwa, wanda aka fara nada shi a shekarar 2021 a zamanin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi aiki a baya a matsayin Shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Kawar da Shan Miyagun Kwayoyi tsakanin 2018 da 2020.
Sabon nadin zai kai tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar har zuwa shekarar 2031.
Marwa wanda ya kasance tsohon gwamnan jihohin Lagos da Borno, ya samu horon soja a Nigerian Military School da kuma Nigerian Defence Academy. Ya rike mukamai da dama cikin rundunar sojin Najeriya, ciki har da Brigade Major na 23 Armoured Brigade da Aide-de-Camp (ADC) ga tsohon Babban Hafsan Soji, Lt.-Gen. Theophilus Danjuma.
Ya kuma yi aiki a matsayin Mataimakin mai bada shawara kan Tsaro a Jakadancin Najeriya da ke Washington DC, da mai bada shawara kan Tsaro ga Wakilan Najeriya a Majalisar Dinkin Duniya.
Marwa na da digiri na biyu a fannin Public and International Affairs daga Jami’ar Pittsburgh (1983–85) da Master of Public Administration daga Jami’ar Harvard (1985–86).
A wa’adinsa na farko, NDLEA ta yi manyan nasarori, ciki har da kama masu safarar miyagun kwayoyi sama da 73,000 da kuma kwace kwayoyi masu nauyin fiye da kilo miliyan 15. Haka kuma hukumar ta gudanar da manyan shirye-shirye kan wayar da kan jama’a game da illolin shan kwayoyi a fadin kasar.
Shugaba Tinubu, a sakonsa, ya bayyana sake nadin a matsayin tabbacin gamsuwa da jajircewar Marwa wajen yaki da fataucin da amfani da miyagun kwayoyi.
“Ina kira gare ka da ka ci gaba da jajircewa wajen fatattakar masu safarar kwayoyi da ke barazana ga makomar al’ummar mu, musamman matasa,” in ji shi.
