Shugaba Tinubu Ya Sanya Hannu Kan Sabuwar Dokar Zabe Ta 2026

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya rattaba hannu a Dokar Zabe ta 2026 (Electoral Act 2026), wanda Majalisar Tarayya ta riga ta amince da ita, a wani muhimmin mataki na tsara yadda za a gudanar da zabukan 2027. 

An yi haka ne da yammacin Laraba 18 ga Fabrairu, 2026 a Fadar Shugaban Kasa, Abuja, inda manyan jami’an Majalisa da ‘yan gwamnati suka halarta. Wannan doka ta maye gurbin Dokar Zabe ta 2022 tare da sabbin gyare-gyare da Majalisar ta amince da su. 

Muhimman Abubuwan Da Sabuwar Doka Ta Duba;
• Lokacin sanar da zabe an rage daga kwanaki 360 zuwa 300 domin kada su hadu da watan azumin Ramadan. 
• An kiyaye tsarin watsa sakamakon zabe ta lantarki, amma akwai sharadin a bar hanyar da ake bi a baya idan babu isasshen sadarwa ta fasaha. 
• Dokar ta shafi tsarin tafiyar da zabuka da kuma wasu kannan dokokin da suka shafi yadda hukumar INEC za ta gudanar da aikinta. 

A halin yanzu, fadar shugaban kasa da Majalisa za su fitar da cikakkun bayanai kan yadda dokar za ta yi aiki a aikace kafin fara tsare-tsaren zaben 2027. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *