Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Nafisa Abdullahi Aminu mai shekaru 17, Rukayya Muhammad Fema mai shekaru 15, da Hadiza Kashim Kalli murna bisa nasarar da suka samu a gasar TeenEagle ta duniya da aka gudanar a birnin London, Ƙasar Ingila. Nafisa ce ta lashe kyautar gwarzon daliba a fannin ƙwarewar harshen Turanci, yayin da Rukayya ta zama ta farko a muhawara, Hadiza kuma ta samu kyautar zinariya a matsayin mai hazaka.
Shugaba Tinubu ya jinjinawa waɗannan matasa na Najeriya da suka ɗaga tutar ƙasa a idon duniya, yana mai cewa wannan nasara alama ce ta hasken makomar ƙasar. Ya kuma yaba da irin gudunmawar cibiyoyin ilimi da gwamnatocin jihohi wajen haɓaka ƙwarewar ɗalibai, yana mai cewa hakan na nuna ingancin tsarin ilimi da ƙasar ke da shi wajen haifar da matasa masu ƙwarewa da basira.
Shugaban ya ƙara jaddada cewa ilimi ginshiƙi ne na ci gaban ƙasa, wanda ya sa gwamnatinsa ke zuba jari a fannin tare da cire ƙalubalen kuɗi ga talakawa masu neman ilimi ta hanyar NELFUND. Ya yi kira ga Nafisa, Rukayya da Hadiza da su ci gaba da jajircewa a karatunsu, yana musu fatan samun karin nasarori a gaba.