Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, murnar cika shekaru 63 a duniya, wanda ya cika ranar 5 ga watan Janairu, 2026.
A cikin saƙon taya murnar da ya fitar, Shugaba Tinubu ya yaba da halayen nagarta da rikon amana da tawali’u da kuma jajircewar Gwamna Yusuf wajen hidimar al’umma, yana mai cewa waɗannan halaye sun bayyana karara a yadda yake tafiyar da harkokin mulkin Jihar Kano.
Tinubu ya bayyana cewa an zaɓi Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Kano a shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), inda kafin hakan ya taɓa riƙe muƙamin Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri daga shekarar 2011 zuwa 2015 a lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
Shugaban ƙasar ya bayyana Kano a matsayin cibiyar siyasar ci gaba a Arewa, yana mai cewa salon mulkin Gwamna Yusuf ya sake jaddada ƙudurorin ci gaban ƙasa da ƙasa (grassroots development) da kuma rage wa talakawa raɗaɗin rayuwa, kamar yadda marigayi Malam Aminu Kano ya assasa tun da dadewa.
A cewar Tinubu:
“Ƙwarewar Gwamna Yusuf a harkokin shugabanci, musamman shekarun da ya yi yana jagorantar manyan ma’aikatun jiha a matsayinsa na kwamishina, sun taimaka masa wajen aiwatar da sauye-sauyen ababen more rayuwa da ake gani a Kano a yau.
“Ya kaddamar da shirye-shiryen sabunta birane, gina gadaje da hanyoyi, ciki har da aikin gina tituna masu tsawon kilomita biyar a kowace ƙaramar hukuma ta jihar.
“Haka kuma na samu labarin cewa ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi da ya yi ta haifar da gagarumin ci gaba a sakamakon ɗaliban Kano a jarrabawar NECO.”
Shugaba Tinubu ya yi wa Gwamnan Kano fatan tsawon rai da ƙarin shekarun jagoranci mai cike da sauye-sauye da alheri ga al’ummar jihar.
