Shugaba Tinubu ya Tura Shettima Zuwa Jihar Kebbi Domin Jajantawa Al’ummar Jihar da Iyayen Yan Matan da aka sace a Maga.
- Shugaban ya sha alwashin kwato su tare da dawo da tsaro a Jihar Kebbi da ƙasa baki ɗaya.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya tura Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zuwa Jihar Kebbi a ranar Laraba domin jajanta wa gwamnatin jihar da iyayen ’yan mata da aka sace daga makarantar sakandaren ’yan mata ta Maga, da kuma tabbatar musu da cewa gwamnati na aiki tukuru don ganin an kubutar da su cikin gaggawa.
A cikin sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, shugaban ya jajanta wa rundunar sojin Najeriya bisa rasuwar sojoji da kuma Birgediya Janar Musa Uba, waɗanda suka rasa rayukansu yayin fafutukar yakar masu ta’addanci a Jihar Borno.
Shugaba Tinubu, wanda aka bayyana cewa an yi masa cikakken bayani kan harin da ya yi sanadin sace ’yan makarantar da kuma harin da ya hallaka sojojin, ya nuna matuƙar damuwa da faruwar lamarin.
Shugaban ya yi Allah-wadai da wannan harin, yana mai kira ga al’ummomi, musamman a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro, da su rika ba hukumomin tsaro bayanan sirri don taimaka musu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Tinubu ya ce hukumomin tsaro ba za su iya yin aiki yadda ya kamata ba matuƙar ba su samun goyon baya da bayanai daga al’ummar yankunan da suke aiki.
