Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci fara gaggauta aiwatar da shirin bayar da kula da lafiya kyauta ga tsofaffin ma’aikata masu ƙaramin albashi da ke karkashin tsarin fansho na Contributory Pension Scheme (CPS). Ya bayyana wannan mataki a matsayin wani muhimmin ɓangare na kare mutuncin rayuwar masu ritaya da samar da kariya ga marasa galihu.
Shugaban ya kuma bayar da umarnin aiwatar da ƙarin kudin fansho da kuma samar da mafi ƙarancin adadin fansho ga tsofaffin ma’aikatan da suka fi fuskantar ƙalubale, domin su samu tallafi na rayuwa mai inganci. Ya bayyana hakan ne bayan ya karɓi bayanin aiki daga Daraktar Hukumar Kula da Fansho ta Ƙasa (PenCom), Ms. Omolola Oloworaran. Shugaban ƙasa ya kuma umarci hukumar ta magance matsalolin da suka dabaibaye batun fanshon ‘yan sanda, yana mai cewa jami’an tsaro da suka sadaukar da rayuwarsu don kare ƙasa, ya kamata su yi ritaya cikin kima da kwanciyar hankali.
A jawabin ta, Daraktar PenCom ta bayyana wa Shugaban ƙasa cewa ana shirin bullo da sabon tsari da zai bai wa ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje damar bayar da gudunmawa cikin tsarin fansho ta hanyar kuɗin ƙasashen waje. Shugaba Tinubu ya yaba da wadannan sauye-sauye, tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da kariya da walwala ga talakawan ƙasa.
