Shugaba Tinubu ya umarci gwamnonin jihohi su ƙyale Kananan Hukumomi Su Samu Yancin cin Gashin kansu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umurci gwamnonin jihohi 36 na ƙasar nan da su tabbatar da cewa suna mika kuɗaɗen Kananan Hukumomi kai tsaye ga hukumomin, domin bin hukuncin Kotun Ƙoli da ya tanadi cikakken ‘yancin kananan hukumomi.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin taron Caucus na Ƙasa na jam’iyyar APC karo na 14, wanda aka gudanar a dakin taro na State House Conference Centre da ke Abuja.

Tinubu ya jaddada cewa ba za a iya samun cikakken ‘yancin kananan hukumomi ba tare da samun kuɗaɗen da za su gudanar da ayyukansu ba, yana mai cewa gwamnatin tarayya za ta tabbatar da cewa ana ba su kuɗinsu kai tsaye kamar yadda Kotun Ƙoli ta tanada.

“‘Yancin Kananan Hukumomi dole ne yayi aiki, ba kawai a rubuce kawai ba, a aikace. Za mu ba ƙananan hukumomi kuɗinsu kai tsaye. Wannan shi ne bin hukuncin Kotun Ƙoli. Ku (Gwamnoni) ɗauki jagoranci da muhimmanci.’”

Shugaban Ƙasar ya kuma buƙaci gwamnonin jihohi da shugabannin jam’iyya da su kasance masu sassauci, jituwa da haɗin kai, tare da shiga harkokin da ke faruwa a jihohinsu har zuwa matakin ƙananan hukumomi, musamman a yankunan karkara.

Dangane da batun tsaro, Tinubu ya bayyana cewa ya tabbatar wa Amurka da Tarayyar Turai cewa Najeriya za ta kafa ‘yan sandan jihohi (State Police) domin tinkarar matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

Ya ce ya nuna kwarin gwiwa cewa hakan zai samu nasara ne saboda yana da jam’iyya da shugabanni da za su mara masa baya wajen cimma wannan buri.

Shugaban Ƙasar ya kuma yi kira ga jam’iyya da shugabanni da su yi amfani da hukuncin Kotun Ƙoli kan Kananan Hukumomi wajen gyara tsarin shugabanci da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya a ƙasar.

Shugaba Tinubu ya buƙaci a ƙara shigar da mata cikin majalisar Caucus, yana mai cewa ya kamata jam’iyya ta tanadi hanyoyin da za su ƙara ba mata dama a matakin yanke shawara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *