Shugaba Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sarkin Zuru

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi jimamin rasuwar Sarkin Zuru, Mai girma Muhammadu Sami (Gomo II), wanda ya rasu a daren Asabar a wani asibiti da ke Landan yana da shekaru 81.

A cikin saƙon ta’aziyya da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja, Shugaban ƙasar ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin babban rashi ga ƙasa baki ɗaya.

Tinubu ya yabawa Sarkin, wanda tsohon janar ne na sojin Najeriya, a matsayin jagora mai kishin ƙasa. Ya tunatar da irin rawar da ya taka a matsayin tsohon gwamnan soja na Jihar Bauchi, inda ya yi ayyukan cigaba da jajircewa.

Shugaban ƙasar ya kuma ambaci jarumtar marigayin a lokacin Yaƙin Basasa, inda ya yi hidima a matsayin matashin jami’i. Ya yaba da jagorancinsa wanda ya samar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a masarautar Zuru da Kebbi gaba ɗaya. Ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama tare da bai wa iyalansa da al’ummar Zuru haƙuri da juriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *