Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga al’ummar Jihar Filato da ‘yan Najeriya baki ɗaya da su zauna lafiya, su haɗa kai don ci gaban ƙasa.
Tinubu ya yi wannan kira ne a yayin bikin jana’izar Marigayiya Nana Lydia Yilwatda, mahaifiyar Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, da aka gudanar a birnin Jos ranar Asabar.
A cikin jawabin nasa, Shugaba Tinubu ya jaddada muhimmancin zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Najeriya, yana mai cewa bambancin addini ko ƙabila bai kamata ya raba ‘yan ƙasa ba.
“Ina addinin Musulunci wanda na gada daga iyayena, ban taɓa canzawa ba. Amma matata Oluremi Fasto ce, kuma tana yi mini addu’a a kowane lokaci. Ban taɓa buƙatar ta sauya addini ba, saboda ina girmama ‘yancin kowane mutum a kan abin da yake bi,” in ji shi.
Shugaban Ƙasar ya kara da cewa, “Mun dogara ne ga Allah guda ɗaya, kuma wurinSa zamu koma domin amsa tambayoyin ayyukanmu da halayenmu. Abin da yafi muhimmanci shi ne kauna da zaman lafiya a tsakaninmu.”
A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Filato, Mista Caleb Mutfwang, ya gode wa Shugaban Ƙasa bisa zuwa domin yin ta’aziyya, duk da cunkoson ayyukansa. Ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ɗauki matakai domin tabbatar da zaman lafiya da daidaituwa a jihar.
Haka kuma, gwamnan ya gode wa Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, bisa tallafin da take bai wa mata da yara marasa galihu a jihar.
Da yake jawabi, Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana mahaifiyarsa a matsayin mace mai ƙwazo, nagarta, da sadaukarwa, wadda ta rayu tana hidima ga al’umma.
Ya gode wa Shugaban Ƙasa, gwamnoni, ‘yan majalisa, da jama’a baki ɗaya bisa goyon baya da ta’aziyya da suka nuna a wannan lokacin na jimami.
Marigayiya Nana Lydia Yilwatda, wadda ta rasu tana da shekaru 83, za a binne ta ne a ƙauyen Dungung dake Ƙaramar Hukumar Kanke a Jihar Filato.