Shugaba Tinubu ya yi kira ga zaman lafiya da tabbatar da tsari a zaɓukan Birnin Tarayya, Jihar Kano da Ribas

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga masu kaɗa ƙuri’a, jami’an tsaro da kuma Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (Independent National Electoral Commission) da su gudanar da kansu cikin tsari da kwanciyar hankali a zaɓukan da za a gudanar a ranar Asabar a Babban Birnin Tarayya (FCT) da jihohin Kano da Ribas.

A wata sanarwa da fadar gwamnati ta fitar, Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa INEC za ta gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomi shida na birnin tarayya, tare da zaɓukan cike giɓi (bye-elections) a mazabun Ahoada East II da Khana II na jihar Ribas, da kuma Kano Municipal da Ungogo a jihar Kano.

Shugaba Tinubu ya ƙarfafa gwiwar dukkan ’yan ƙasa masu katin zaɓe da su fito su kaɗa ƙuri’unsu ba tare da tsoro ba, yana mai jaddada cewa dimokuraɗiyya na bunƙasa ne a yanayi na natsuwa, haƙuri da girmama juna.

Ya kuma yi kira ga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da magoya bayansu da su guji tashin hankali, kalaman tayar da fitina da duk wani abu da zai iya raunana sahihancin tsarin zaɓen. Shugaban Ƙasar ya gargaɗi duk wani nau’i na danniya, tsoratarwa ko matakan da za su hana ’yan ƙasa amfani da haƙƙinsu na zaɓe, yana mai jaddada cewa aikin jami’an tsaro shi ne kare rayuka da dukiyoyi tare da kiyaye tsarkin ƙuri’a.

Haka nan, Shugaban Ƙasar ya buƙaci INEC da ta ɗauki dukkan matakan da suka dace domin ƙarfafa amincewar masu zaɓe, ta hanyar tabbatar da tantance masu kaɗa ƙuri’a a kan lokaci, gudanar da kaɗa ƙuri’a cikin sauƙi, tattara sakamako yadda ya dace, da tura sakamakon cikin gaggawa, bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026.

A cewarsa, gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancinsa za ta ci gaba da tallafa wa dukkan hukumomin da ke da alhakin tabbatar da sahihan zaɓe masu ’yanci da adalci. Ya kuma yaba wa mazauna Birnin Tarayya, Kano da Ribas kan wayewarsu ta dimokuraɗiyya, yana mai nuna ƙwarin gwiwar cewa zaɓukan za su bayyana ainihin muradin jama’a tare da ƙara ƙarfafa tafiyar dimokuraɗiyyar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *