Shugaba Tinubu ya yi maraba da dawowar dalibai 100 na Papiri, ya umurci jami’an tsaro su gaggauta ceto sauran

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa hukumomin tsaro bisa jajircewarsu da ya kai ga kubutar da dalibai 100 na makarantar Papiri Catholic School da ke jihar Neja, waɗanda aka sace a ranar 21 ga Nuwamba.

A cikin wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, Tinubu ya ce yana murna da dawowar yaran cikin koshin lafiya, tare da yin kira ga jami’an tsaro su hanzarta ceto sauran dalibai 115 da malaman makarantar da har yanzu ke tsare a hannun masu garkuwa da mutane.

Shugaban kasan ya ce gwamnatin tarayya na aiki kafada da kafada da gwamnatin jihar Neja domin ganin an dawo da dukkan yaran zuwa ga iyalansu ba tare da wani lahani ba.

“Ina murna da jin cewa an dawo da dalibai 100 na makarantar Catholic da ke jihar Neja. Na taya Gwamna Umar Bago murna, kana ina yaba wa hukumomin tsaro bisa jajircewar da suka nuna wajen tabbatar da dawowar yaran tun bayan faruwar lamarin,” in ji Shugaba Tinubu.

Ya kara da cewa umarninsa ga hukumomin tsaro ba ya canzawa: cewa dole ne a kubutar da dukkan daliban da sauran ’yan Najeriya da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan.

“Dole ne mu tabbatar ba a rasa ko guda ba. Gwamnatin tarayya za ta ci gaba da aiki da gwamnatin Neja da sauran jihohi domin kara tsaro a makarantunmu, tare da samar da muhalli mai aminci ga yaranmu,” in ji shugaban kasan.

Tinubu ya kuma jaddada cewa daga yanzu dole ne hukumomin tsaro tare da gwamnonin jihohi su dauki matakan da za su dakile sake afkuwar irin wadannan hare-hare.

“Ba za mu kara yarda da yanayin da yara ke zama abin farin dango a hannun ’yan ta’adda ba. Ya isa haka. Dole mu kare su daga duk wani yunƙurin karya musu karatu da jefa iyayensu cikin tashin hankali,” in ji Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *