Shugaba Tinubu ya yi matuƙar jimamin rasuwar babban malami, Sheikh Dahiru Bauchi

Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matuƙar alhini kan rasuwar babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wanda ya rasu a ranar Alhamis yana da shekaru 101.

A cikin wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu ya ce rasuwar Sheikh Dahiru babban rashi ne ba kawai ga iyalai da mabiyansa ba, har ma ga ƙasar gaba ɗaya, yana mai jaddada cewa marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen shiryar da al’umma zuwa ga tafarkin gaskiya.

Shugaban ya bayyana Sheikh Dahiru Bauchi a matsayin jagoran Darikar Tijjaniyya da ya yi fice wajen wa’azi, karantarwa da kuma yaɗa zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Ya ce: “Sheikh Dahiru Bauchi malami ne, uba, kuma muryar da ke kira da hikima da natsuwa. A matsayin fitaccen mai tafsirin Alƙur’ani, ya kasance ginshiƙi wajen ƙarfafa zaman lafiya da tsoron Allah. Mutuwarsa ta bar gibi mai faɗi a wannan fage.”

Shugaba Tinubu ya kuma tuna da addu’o’i da goyon bayan da Sheikh Dahiru ya ba shi a lokacin yaƙin neman zaɓen 2023.

Shugaban ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, mabiyansa da dukkan al’ummar Musulmi a cikin ƙasar da waje. Ya roƙe su da su ci gaba da ɗaukaka sunan marigayin ta hanyar bin koyarwarsa ta zaman lafiya, kyautata zamantakewa da ƙarfafa kusanci da Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *