Shugaba Bola Tinubu zai kai ziyarar aiki ta yini guda zuwa Jihar Adamawa a ranar Litinin, kasa da awanni 48 bayan makamanciyar ziyarar da ya kai Jihar Kebbi.
A yayin ziyarar, Shugaban kasar zai kaddamar da wasu muhimman ayyuka da aka kammala tare da ganawa da manyan jami’an gwamnati da kuma sarakunan gargajiya na jihar.
Daga cikin ayyukan da aka shirya kaddamarwa a birnin Yola da Jimeta akwai titin Galadima Aminu mai layi takwas da ke hada Gimba da babban birnin jihar. Haka kuma, Shugaban zai kaddamar da makarantar zamani da ta kunshi matakan firamare, kananan makarantun gaba da firamare, da kuma karamar sakandare.
Sauran ayyukan sun hada da sabon babban dakin taruka mai bangarori da dama, kotun koli da aka sake gyarawa, sabon ginin gidajen jami’ai, da kuma gyaran Fadar Gwamnati.
Bayan kammala kaddamar da ayyukan da ganawar da zai yi da al’ummar jihar, Shugaba Tinubu zai koma Abuja.
