Gwamna Abba ya yi fusata da yadda aikin raba abincin azumi ke gudana a birnin Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano, ya nuna ɓacin ran sa ganin yadda ake tafiyar da aikin dafawa, rabawa da kuma rashin ingancin abincin azumi ke gudana a cikin birnin Kano. Cikin wata sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitara ranar Juma’a, Gwamna Abba ya ce bai ji daɗin…
