SHUGABAN KASA TINUBU YA YI ALHININ RASHIN MALAM MAINASARA HABIBI
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matukar kaɗuwarsa bisa rasuwar babban malamin addinin Islama na garin Zariya, Sheikh Mainasara Liman Habibi. Sheikh Habibi ya rasu a karshen makon da ya gabata yana da shekaru 67. A lokacin rayuwarsa, malamin ya kasance shugaban masu wa’azi na kungiyar Fityanul Islam ta kasa wadda kungiya ce ta…
