Gwamnatin Tarayya za ta goyi bayan shirin fim kan tarihin shekaru 25 na dimokiraɗiyyar Nijeriya
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa za ta ba da cikakken goyon baya ga samar da wani shirin fim mai nuna tarihin shekaru 25 na mulkin dimokiraɗiyya a Nijeriya. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabannin Majalisar Tuntuɓa ta Jam’iyyun Siyasa,…
