Dole ne mu daina barin bambancin addini da ƙabilanci yana raba kan mu a matsayin mu na ‘yan ƙasa, inji Ministan Yaɗa Labarai
Wata tabbatacciyar hanya ta samun haɗin kan ‘yan Nijeriya wadda ba ta bari bambancin ƙabilanci, addini, da siyasa ya raba kan mu ba ita ce ta samar da wani labari mai ban sha’awa na ƙasa, mai ƙarfafa amana da amincewa a tsakanin ‘yan Nijeriya, inji Alhaji Mohammed Idris, Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai….
