Gwamnan Zamfara ya halarci hawan sallah a Ƙauran Namoda
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya halarci bikin hawan Durbar a Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a ranar Lahadin nan. Masarautar Ƙauran Namoda na gudanar da wani gagarumin biki na musamman bayan Sallar Idi, wanda aka fi sani da Hawan Durbar duk shekara. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris,…
