Nijeriya za ta ƙarfafa alaƙa da Indonesiya a taron ƙasar da Afirka karo na biyu
Gwamnatin Nijeriya za ta ƙarfafa hulɗar da ke tsakanin ta da Indonesiya yayin da aka fara taron ƙasar da nahiyar Afirka karo na biyu a birnin Bali na ƙasar Indonesiya. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda yanzu haka yake Indonesiya domin wakiltar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin Shugaban…
