Gwamnatin Najeriya ta bayyana kuɓutar da ɗalibai mata 24 na Sakandiren Maga a Jihar Kebbi
Hukumomin Najeriya sun tabbatar da kuɓutar da dalibai mata 24 na makarantar sakandire da ke garin Maga, Jihar Kebbi, waɗanda ‘yan bindiga suka sace a makon da ya gabata. Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya sanyawa hannu, ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi farinciki da dawowar daliban,…
