Sama da mutane miliyan 7.4 suka bar muhallansu sakamakon yaki a kasar Sudan – majalisar dinkin duniya
Ofishin kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya (OCHA) ya bayyana cewa yawan mutanen da suka bar muhallansu a Sudan sakamakon yaki ya haura miliyan 7,400,000. “Sama da mutane miliyan 7.4 suka bar muhallansu a ciki da zuwa wajen Sudan tun bayan da yaki ya barke a tsakanin sojojin kasar Sudan (SAF) da…
