Shugaba Tinubu ya umarci kwamitin majalisar zartarwa ta ƙasa da ya gaggauta daukar matakin rage farashin abinci a ƙasar.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya umarci kwamitin majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) da ya gaggauta ɗaukar matakan da za su saukar da farashin abinci a faɗin ƙasar. Ƙaramin Ministan Noma da Tsaron Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Laraba, inda ya ce shugaba Tinubu ya bayar da umarnin tabbatar…
