Sakkwatawa Ba Sa Goyon Bayan Kudurin Dokar Rage Karfin Sarkin Musulmi
Sakkwatawan da suka halarci zaman sauraron ra’ayin jama’a akan kudurin dokar yiwa masarautar Mai alfarma Sarkin musulmi gyaran fuska da majalisar dokokin ta gabatar sun nuna adawa da kyamar wannan dokar. Da yawa daga wakilan al’umma da suka halarci wannan zaman sun koka da rashin basu damar su bayyana ra’ayin su game da wannan dokar….
