Makiyaya hudu sun rasu bayan cin kifin da ake zargin na dauke da guba a Taraba
Fulani makiyaya mutum hudu da aka bayyana sunansu da Abdul Juli, Sule Abubakar, Adamu Mato da Saidu Payo sun rasu a karamar hukumar Takum da ke jihar Taraba bayan ruwaito cewa sun dafa tare da cin kifin da suka tsinta a bakin ruwan rafin Kashimbila yayin da suke yin kiwo, kamar yadda rahoton PM News…
