Wata Yarinya Ta Zama Mataimakiyar Shugaban Najeriya Ta Rana Daya
Da yake jawabi yayin ganawarsa da tawagar PLAN International karkashin jagorancin Daraktar inganta fasahar kirkire-kirkire ta kungiyar, Helen Mfonobong Idiong a ranar Litinin, Sanata Kashim Shettima ya gayyaci wata matashiya, Joy Ogah, don ta zauna a kan karagar Mataimakin Shugaban Kasa ta yi jawabi ga al’ummar kasa kan kudiri inganta hakkokin ƴaƴa mata Mataimakin Shugaban…
