Sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC na nuna raunin jam’iyyun adawa — Shettima
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya ce yawaitar sauya sheka daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar APC na bayyana raunin da ke cikin jam’iyyun adawa, yayin da APC ke ƙara ƙarfi. Shettima ya bayyana haka ne a Enugu, inda ya wakilci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a taron maraba da Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu,…
