Tinubu Ya Buƙaci Ƙarin Haɗin Kai Yayin Da Nijeriya Ke Cika Shekara 65 da Samun ’Yancin Kai
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su zauna cikin haɗin kai da zaman lafiya domin cigaban ƙasa baki ɗaya. Wata sanarwa da Dakta Suleiman Haruna, Daraktan Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, ya sanya wa hannu, ta ce Shugaban Ƙasar ya bayyana hakan ne…
