Sauye-sauyen Tinubu Suna Taimaka Wa Farfaɗowar Tattalin Arzikin Nijeriya — Minista
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya na samun cigaba sannu a hankali, inda ya danganta hakan da sauye-sauyen da ake aiwatarwa a fannoni daban-daban ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu. Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja, yayin da yake karɓar baƙuncin mambobi…
