Gwamnati ba ta musanya sunan Titin Murtala Muhammed da na Soyinka ba, inji Minista
Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata ji-ta-ji-tar da ake yaɗawa cewa wai ta canza sunan Titin Murtala Muhammed da ke Abuja zuwa Titin Wole Soyinka. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Rabiu Ibrahim, mataimakin sa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, ya saki…
