Ku cusa ɗabi’u nagari a zukatan ‘ya’yan ku, kiran Ministan Yaɗa Labarai ga iyaye
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su jajirce wajen ganin sun cusa halaye masu kyau a zukatan ‘ya’yan su. A wata sanarwa da Mataimaki na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai na ministan, Malam Rabiu Ibrahim, ya fitar a ranar Lahadi,…
